Wanda Malam (H) ya karanci tafsirin al-kur'ani mai tsarki a wajensa da kuma shaikh isa wazikiri shi kuma da Malam (H) ya karanci wadansu fannoni na ilmukan addini a wa jensa. Haka kuma akwai Malam Ibrahim balarabe. Malam dai ya kammala karatunsa a makarantar (SAS) a kano a shekara 1975.
karatun Malam (H) Na zamani A (SAS) kano ne Malam ya soma karatunsa na zamani (wato boko). A nan ne kuma basirar Malam da allah (S W T) ya hore masa da kuma hazakarsa ta bayyana ainun.
A lokacin ne Malam (H) yasoma koyon darussan boko, Yakuma yi saurin cimma sauran dalibai wadanda sukayi karatun (primary) da kuma fahimtar darussan da gaggawa ta fuskacin kwakwalkwarsa dakuma kokarin sa.
Har dai a karshe Malam (H) ya kasance shine mafi kokari da hazaka a tsakanin dalibai akusan dukkanin darussan da'ake koyarwa dasu a cikin aji. Wannan kuma sai ya haifar da dankon zumunci mai yawa a tsakanin Malam (H) da kuma sauran Dalibai. kusan daliban sukan kewaye Malam (H) suna neman Karin fahimtar darussan da'ake koya masu daga wurin sa
.
A lokacin da Malam (H) yake daukan jarabawar karshe ta grade 2 ,akusan lokacin ne kuma ya zaunawa daukar jarabawar GCE ta kebe.
A jarrabawar GCE ta kebe Malam ya dauki darussan da suka hada tattalin arziki (economics), gwamnati (government), Hausa dakuma musulumci (Islamic studies). Da yake sakamakon jarrabawowin Malam (H) sunyi kyau kwarai da gaske, wannan ya bai wa Malam damar samun gurbin karatu Kai tsaye a jami'ar Ahmad Bello dake samaru -zariya a shekarar karatu ta 1976/77 A can ne kuma Malam (H) ya karanci bangaren tattalin arziki Malam kuma yaka rasa karatun sa a shekara 1997. Duk kuma dayeke cewa Malam yasamu sakamako mai daraja ta daya a lokacin daya karussa karatun nasa a jami'ar, amma duk dahaka hukumar jami'ar tahana Malam (H) takardun shaidar karatun sa asa bili da wani dalili wadda hukumar ta baiwa kanta sani.
Amma tabbas dalilin bazai rasa nasaba ba da kokarin da Malam (H) yayi na'aza tobalin gwagwarmayar addini daga jami'ar ta Ahmadu Bello gwagwarmayar data samu tasisri ainun, a jami'ar har ta kai ga cewa tarihin jami'ar ba zai taba yin dai dai ba idan ba'a fada da ita ba.
hazakar Malam (H) tun farko nayi bayani cewa Malam mutum ne da Allah (S W T) ya azurta da basira da kwakwalwa dakuma hazaka mai yawan gaske tun alokacin hai wuwar sa.Malam yakasan ce yana da hardace duk karatuttukan da yakeyi a zaurakun karatu.
Mun kuma kara muna cewa Malam yakarance kusan dukka nin litattafan mukaddama na fanno nin ilmukan addini tun kafin ya girma. Mun kuma kawo cewa Malam (H) ya San tafsirin al-qur'ani mai starki tun kan ya balaga.
.
Karin haske dazamu yi a wannan rubutu shine na muna cewa Malam (H) yana da kokarin rubuce-rubucen liattafai (wato juya littafai )tun yana saurayinsa. Ya kasance yakanyi rubutu a kusan kowane dare. Ta hakane yake rubuce wa"yan su litattafan da ke da stada da kuma wuyar samu a lokacin don amfani dasu a karan-kansa a zaurakun karatu. Ta haka ne kuma Malam (H) ya samu saukin samun wadansu litattafai wadanda yayi karatu da su a zaurukan karatu.